Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:13
9 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.


A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.


Nan da nan kuwa Ariyok ya kai Daniyel gaban sarki, ya ce masa, “Na sami wani daga cikin kamammun ƙasar Yahuza wanda zai iya sanar wa sarki da fassarar.”


Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.


Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”


A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa.


Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda ubana ya kawo daga Yahuza?


har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”


Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan