Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 6:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Sai mutanen nan suka tafi, suka iske Daniyel yana kai koke-kokensa da roƙonsa ga Allahnsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 6:11
7 Iomraidhean Croise  

Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,


Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki. Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama, Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!


A kowace rana nakan gode maka sau bakwai, Saboda shari'unka masu adalci ne.


Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako, Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.


Ku waɗanda kuka tsere wa takobi! Ku gudu! Kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a can nesa inda kuke, Ku kuma yi ta tunawa da Urushalima.


Sa'an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan