Daniyel 5:7 - Littafi Mai Tsarki7 Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20207 Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Faic an caibideil |