Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 5:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Nan da nan sai yatsotsin hannun mutum suka bayyana, suka yi rubutu a kan shafen bangon fādar sarkin, wanda yake daura da fitila. Sarki kuwa yana ganin hannun sa'ad da hannun yake rubutu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 5:5
15 Iomraidhean Croise  

Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.


Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.


Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda.


Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.


Nan take sai abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar ya tabbata. Aka kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, akaifunsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.


Yanzun nan aka kawo mini masu hikima, da masu dabo don su karanta wannan rubutu, su kuma bayyana mini ma'anarsa, amma sun kāsa faɗar ma'anar rubutun.


Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse.


Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.


Sai dukan masu hikima na sarki suka shigo, amma ba wanda ya iya karanta rubutun balle ya faɗa wa sarki ma'anarsa.


ya kuma yanke igiyar nan ta Shari'a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyensa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan