Daniyel 5:4 - Littafi Mai Tsarki4 Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20204 Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse. Faic an caibideil |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.