Ku wasa kibau, ku cika kwaruruwanku! Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan Mediyawa, Domin yana niyyar hallaka Babila. Gama Ubangiji zai yi ramuwa saboda Haikalinsa.
“Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta, Da masu mulkinta, da shugabanninta, Da sojojinta su sha su yi maye. Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna.