Daniyel 5:3 - Littafi Mai Tsarki3 Sai suka kawo tasoshin zinariya da na azurfa waɗanda aka kwaso daga cikin Haikali, wato Haikalin Allah a Urushalima. Sai sarki da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa, suka yi ta sha da su. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20203 Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Faic an caibideil |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.