Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da suke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”
Na ga wahayi na waɗansu mugayen abubuwa, wato na cin amana da hallakarwa. Rundunar sojojin Elam, ku kama yaƙi! Rundunar sojojin Mediya ku kewaye birane da yaƙi. Allah zai kawar da wahalar da Babila ta haddasa.
Duk da haka bala'i zai auko miki, Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba, Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya, Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!
Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al'umman nan.