Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 5:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Ma'anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene , Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 5:26
11 Iomraidhean Croise  

Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma? Amma zan jira lokaci mafi kyau, In jira sai lokacin wahala ya wuce.


Ubangiji ya ce “Ina zuga mutanen Mediya, don su faɗa wa Babila da yaƙi. Ba su kula da azurfa ba, ba kuwa za a jarabce su da zinariya ba.


Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.


Wannan shi ne rubutun da aka yi, MENE, MENE, TEKEL, da UPHARSIN.


a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.


Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan