Sai annabi Iliya ya rubuta masa wasiƙa ya ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na tsohonka Dawuda ya ce, ‘Da yake ba ka bi halin tsohonka Yehoshafat ba, da halin Asa Sarkin Yahuza,
Duk da haka bala'i zai auko miki, Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba, Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya, Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!
Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.
Banda haka kuma Ubangiji zai ba da Isra'ilawa tare da kai a hannun Filistiyawa. Gobe, da kai da 'ya'yanka maza za ku kasance tare da ni. Ubangiji zai ba da rundunar yaƙin Isra'ila a hannun Filistiyawa.”