Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 5:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 5:20
27 Iomraidhean Croise  

Duk da haka suka ƙi kasa kunne, suka taurare zuciyarsu kamar yadda kakanninsu suka yi, waɗanda ba su yi imani da Ubangiji Allahnsu ba.


Amma Hezekiya bai nuna godiya a kan amfanin da ya samu ba, saboda girmankai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuza da Urushalima.


Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra'ila.


Yanzu na sani Ubangiji yake gāba da sauran alloli duka, gama ya ceci Isra'ilawa daga tsanantawar da Masarawa suka yi musu.”


Har yanzu kana fariya a kan jama'ata, ba ka sake su ba.


Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.


Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.


Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.


Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Ka faɗa wa sarki da sarauniya, uwarsa, su sauka daga gadon sarautarsu, Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin sarautarsu daga kansu.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.’ ”


Ku da kuke zaune a Dibon, Ku sauka daga wurin zamanku mai daraja, Ku zauna a busasshiyar ƙasa, Gama mai hallaka Mowab ya zo ya yi gab da ku. Ya riga ya rushe kagararku.


Ubangiji ya ce, “Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi. Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.


“Domin haka Ubangiji Allah ya ce, Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa,


“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.


Kamar yadda aka umarta a bar kututturen itacen da saiwoyinsa, haka nan za a tabbatar maka da sarautarka sa'ad da ka gane Mai Sama ne yake mulki.


Wannan duka kuwa ya sami sarki Nebukadnezzar.


Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”


Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.


Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”


Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya muddin akwai “Yau”, don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi.


Don me za ku taurare zukatanku kamar yadda Masarawa da Fir'auna suka taurare zukatansu? Sai da Allah ya wahalshe su tukuna kafin su sallami Isra'ilawa su tafi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan