Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 5:18 - Littafi Mai Tsarki

18 “Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 5:18
25 Iomraidhean Croise  

Ya yi masa magana mai kyau, ya kuma ba shi matsayi fiye da sarakunan da suke tare da shi a Babila.


A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka, Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.


Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa, Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.


Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai, Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!


Gama kai, ya Ubangiji, Maɗaukaki ne har abada.


zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.


‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.


Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.


Bai kuma yarda a hana wa mutum hakkinsa A gaban Maɗaukaki ba,


Ba daga bakin Maɗaukaki Alheri da mugunta suke fitowa ne ba?


zan bashe shi a hannun mai ƙarfi, a cikin al'ummai. Zai sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na fitar da shi.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.


Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.


Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”


“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.


Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Allahna ya aiko mala'ikansa ya rufe bakunan zakoki, ba su iya yi mini lahani ba, domin ban yi wa Allah laifi ba, ban kuma yi maka ba.”


da rana a tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata.


“Saboda haka, ya sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba.


Duk da haka Maɗaukaki ba ya zama a gidaje, ginin mutum. Yadda Annabi Ishaya ya ce,


Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu, Sa'ad da ya raba 'yan adam, Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan