Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 5:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Daniyel kuwa ya amsa, ya ce wa sarki, “Riƙe kyautarka, ka ba wani duk da haka zan karanta wa sarki rubutun, in kuma bayyana masa ma'anarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 5:17
8 Iomraidhean Croise  

cewa ba zan ɗauki ko da zare ɗaya ko maɗaurin takalmi ba, ko kowane abin da yake naka, domin kada ka ce, ‘Na arzuta Abram.’


Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.” Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”


Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.” Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.


Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba, sa'ad da mutumin ya juyo daga karusarsa don ya tarye ka? Wannan shi ne lokacin karɓar kuɗi, da riguna, da gonaki na zaitun, da na inabi, da tumaki, da shanu, da barori mata da maza?


Zan hurta umarnanka ga sarakuna, Ba kuwa zan ji kunya ba.


Amma idan kun tuna mini mafarkin, duk da fassararsa, to, zan ba ku lada, da kyautai, da girma mai yawa. Don haka sai ku faɗa mini mafarkin, duk da fassararsa.”


Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.


Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan