Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 5:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda ubana ya kawo daga Yahuza?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 5:13
20 Iomraidhean Croise  

Waɗanda suka komo daga zaman talala kuwa suka yi haka. Sai Ezra firist ya zaɓi mutanen da suke shugabannin gidajen kakanninsu. Aka rubuta sunan kowa. Sai suka taru ran ɗaya ga watan goma, don su bincika al'amarin.


Sai aka yi shela a dukan Yahuza da Urushalima, cewa dukan waɗanda suka komo daga zaman talala, su hallara a Urushalima.


Sa'ad da abokan gāban Yahuza da Biliyaminu suka ji waɗanda suka komo daga bauta suna gina Haikalin Ubangiji Allah na Isra'ila,


Sai mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da sauran waɗanda suka komo daga bauta, suka yi bikin keɓe Haikalin Allah da murna.


A shekara ta uku ta mulkin Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo Urushalima ya kewaye ta da yaƙi.


Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.


Daniyel kuwa ya ci gaba har shekarar farko ta sarki Sairas.


A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.


Nan da nan kuwa Ariyok ya kai Daniyel gaban sarki, ya ce masa, “Na sami wani daga cikin kamammun ƙasar Yahuza wanda zai iya sanar wa sarki da fassarar.”


Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.


Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba.


Na ji labari, cewa kana da ruhun alloli tsarkaka, da fahimi, da ganewa, da mafificiyar hikima.


“Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba.


Da Belshazzar ya kurɓa ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezzar ubansa ya kwaso daga Haikali a Urushalima, domin sarki, da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa su sha ruwan inabi da su.


Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”


A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari.


Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.


Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi.


Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan