Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 ‘Ya Belteshazzar shugaban masu sihiri, tun da yake na san ruhun alloli tsarkaka yana a cikinka, ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga mafarkin da na yi, sai ka faɗa mini fassararsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:9
18 Iomraidhean Croise  

Sai Fir'auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”


Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare.


Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki. Za ki tsira daga shan zalunci da razana. Gama ba za su kusace ki ba.


A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shi Don ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya, Ya zama itacen al'ul na gaske. Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa, Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.


Lalle ka fi Daniyel hikima, Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.


A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.


“Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.”


Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni.


Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce,


Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba.


Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan