Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:36 - Littafi Mai Tsarki

36 “A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. 'Yan majalisata da fādawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

36 A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:36
11 Iomraidhean Croise  

Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.


Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali'u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.


“Ya sarki, ka ga wani babban mutum-mutum mai walƙiya, mai bantsoro, yana tsaye a gabanka.


kai ne wannan itace, ya sarki. Ka yi girma, ka ƙasaita. Girmanka ya kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko'ina a duniya.


Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”


“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.


Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.


Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan