Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Dukan mutanen duniya ba a bakin kome suke ba. Yakan yi abin da ya gamshe shi da ikokin sama da kuma na mutanen duniya. Babu mai hana shi ko yă ce masa; “Me ka yi?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:35
41 Iomraidhean Croise  

“Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi, Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata.


Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi? Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa, Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum?


“Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka? Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”


“Na sani kai kake da ikon yin dukan abu, Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.


Allah mai hikima ne, mai iko, Ba wanda zai iya ja in ja da shi.


Allahnmu yana Sama, Yana aikata yadda yake so.


Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya, A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.


Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.


“Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina! Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne. Hakika duk mutum mai rai, Bai fi shaƙar iska ba.


Ku ji wannan, ko wannenku, Ku saurara jama'a duka na ko'ina,


Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.


Da iko sarki yake aiki, don haka ba mai iya ce masa, “Don me?”


Mutanen Masar za su firgita saboda Yahuza, kowane lokaci za su tuna da ƙaddarar da Ubangiji Mai Runduna ya shirya dominsu.


Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya. Sa'ad da kake yi wa duniya da jama'arta shari'a Dukansu za su san yadda adalci yake.


Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur, Ba wanda zai iya tserewa daga ikona, Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”


Yakan yi ceto, yakan kuma kuɓutar, Yana aikata alamu da mu'ujizai a sama da duniya. Shi ne wanda ya ceci Daniyel daga bakin zakoki.”


Suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Ya Ubangiji, muna roƙonka kada ka bar mu mu halaka saboda ran mutumin nan, kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka yi abin da ya gamshe ka.”


Tun da yake Allah ya yi musu baiwa daidai da wadda ya yi mana, sa'ad da muka gaskata da Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni in dage wa Allah!”


Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.


amma in na Allah ne, ba dama ku rushe su. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.”


Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.


Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?


“Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.


A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,


Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da daddare domin su bincike ƙasar.”


Sama'ila kuwa ya faɗa masa kome da kome, bai ɓoye masa kome ba. Sai Eli ya ce, “Ai, Ubangiji ne, bari ya yi abin da ya yi masa daidai.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan