Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Nan take sai abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar ya tabbata. Aka kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, akaifunsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:33
7 Iomraidhean Croise  

Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.


Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami 'yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”


Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”


Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Nan da nan sai yatsotsin hannun mutum suka bayyana, suka yi rubutu a kan shafen bangon fādar sarkin, wanda yake daura da fitila. Sarki kuwa yana ganin hannun sa'ad da hannun yake rubutu.


Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan