Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:32
22 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da ya yi addu'a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa'an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.


“Na sani kai kake da ikon yin dukan abu, Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.


Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi, Ba wanda yake tambayarsa cewa, ‘Me kake yi?’


Allahnmu yana Sama, Yana aikata yadda yake so.


Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya, A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.


Fir'auna ya ce, “Gobe ne.” Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.


A wannan karo, ni da kaina zan kawo maka, da fādawanka, da jama'arka annoba, domin ka sani babu mai kama da ni a dukan duniya.


Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu'a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce.


Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”


Al'ummai ba kome ba ne a wurin Ubangiji, Ba su fi ɗigon ruwa ba, Manisantan tsibirai ba su fi ƙura nauyi ba.


Al'ummai ba kome ba ne ko kaɗan a gare shi.


Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare, Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji, Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.


‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.


Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan