Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:30 - Littafi Mai Tsarki

30 sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:30
33 Iomraidhean Croise  

Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke.


Sai ya nuna wadatar mulkinsa, da martabarsa, da darajarsa har kwanaki masu yawa, wato kwana ɗari da tamanin.


Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ya Ubangiji Allahna, mai girma ne kai! Kana saye da ɗaukaka da daraja,


Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba, Zai mutu kamar dabba.


Sukan yi wa waɗansu ba'a, Suna faɗar mugayen abubuwa, Masu girmankai ne su, suna shawara A kan yadda za su zalunci waɗansu.


Masu girmankai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa.


Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Daular Babila ita ce mafi kyau duka, abin fāriya ce ga jama'arta. Amma ni Ubangiji, zan kaɓantar da ita kamar yadda na yi da Saduma da Gwamrata!


“Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar, Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna, Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.


Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.


Sukan wuce da sauri kamar iska, Su yi tafiyarsu. Su masu laifi ne, Ƙarfinsu shi ne gunkinsu.”


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”


wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci.


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”


Sai kuma mala'ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ita da ta zuga dukkan al'ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”


Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al'ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.


A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”


za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce, “Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni! Ya kai birni mai ƙarfi, Babila! A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”


Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce, “Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan