Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:3 - Littafi Mai Tsarki

3 “Alamunsa da girma suke! Al'ajabansa da bantsoro suke! Sarautarsa ta har abada ce, Mulkinsa kuma daga zamani zuwa zamani ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Alamunsa da girma suke, ayyukansa da girma suke! Mulkinsa mulki ne na har abada; sarautarsa kuma za tă dawwama daga zamani zuwa zamani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:3
29 Iomraidhean Croise  

“Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa, A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.


Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa! Da hikima ƙwarai ka halicce su! Duniya cike take da talikanka.


Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah, Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.


Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada.


Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa, Yana duban al'ummai, Don kada 'yan tawaye su tayar masa!


Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila, Wanda shi kaɗai ne yake aikata al'amuran nan masu banmamaki!


Ka yi tafiya a teku, Ka haye teku mai zurfi, Amma ba a ga shaida inda ka taka ba.


Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah, Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.


Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji! Tunaninka da zurfi suke!


Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka. Ka aikata al'amura masu banmamaki, Ka tafiyar da su da aminci, Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.


Dukan wannan hikima daga wurin Ubangiji Mai Runduna ne. Shirye-shiryen da Allah ya yi na hikima ne kullum kuwa sukan yi nasara!


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.


Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”


Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’


Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!


Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?


Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.


Amma a game da ɗan, sai ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne, Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya.


sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.


Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan