Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Kamar yadda aka umarta a bar kututturen itacen da saiwoyinsa, haka nan za a tabbatar maka da sarautarka sa'ad da ka gane Mai Sama ne yake mulki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:26
13 Iomraidhean Croise  

Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila.


Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daga nan Daniyel ya yabi Allah na Sama.


Ya sarki, kai ne sarkin sarakuna wanda Allah na Sama ya ba ka sarauta, da iko, da ƙarfi, da daraja.


Amma a bar kututturen da saiwoyinsa a ƙasa Ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. A bar shi can cikin ɗanyar ciyawar saura, Ya jiƙe da raɓa, Ya yi ta cin ciyawa tare da namomin jeji.


Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.


Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.


Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”


Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.


Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”


Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah,


Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka.


Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan