Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:25
15 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama, Shi yake sarautar duka.


Suka musaya ɗaukakar Allah Da siffar dabba mai cin ciyawa.


Allah yake yin shari'a, Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu.


Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji, Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!


‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


Ya sarki, kai ne sarkin sarakuna wanda Allah na Sama ya ba ka sarauta, da iko, da ƙarfi, da daraja.


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


A raba shi da hankali irin na mutane, A ba shi irin na dabba. Zai zauna a wannan hali har shekara bakwai.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan