Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:24 - Littafi Mai Tsarki

24 “Ga ma'anarsa, ya sarki, wannan ƙaddara ce wadda Maɗaukaki zai aukar wa shugabana sarki da ita.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 “Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:24
14 Iomraidhean Croise  

“Wannan ita ce ƙaddarar mugaye, Wadda Allah ya ƙayyade musu.”


Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama'arsa. Ya sa su suka yi ta kai da kawowa A hamada inda ba hanya.


Ta wurin umarninsa aka kafa su A wurarensu har abada, Ba su kuwa da ikon ƙi.


Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta. Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne, Yau ne na zama mahaifinka.


Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.


Sarki zai zauna dafa'an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.


Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.


Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan