Daniyel 4:23 - Littafi Mai Tsarki23 Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202023 “Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’ Faic an caibideil |
Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”