Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:22 - Littafi Mai Tsarki

22 kai ne wannan itace, ya sarki. Ka yi girma, ka ƙasaita. Girmanka ya kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko'ina a duniya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:22
18 Iomraidhean Croise  

Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.”


Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!


Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra'ila, na cece ka daga hannun Saul.


Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama.


Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai, Amincinka kuma ya kai sararin sammai.


Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji, Ta kai har sammai, Amincinka ya kai sararin sammai.


‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.


Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


“ ‘Itacen ya yi girma, ya ƙasaita, Ƙwanƙolinsa ya kai har sama, Ana iya ganinsa ko'ina a duniya.


yana da ganyaye masu kyau da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci, namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, tsuntsaye kuma suka zauna a rassansa,


Bayan wata goma sha biyu, sa'ad da yake yawatawa a kan benen fādar Babila,


“A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. 'Yan majalisata da fādawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā.


Don dā ma Yahaya ya ce masa bai halatta ya zauna da ita ba.


Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama, Allah kuwa ya tuna da laifofinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan