Daniyel 4:19 - Littafi Mai Tsarki19 Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202019 Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan! Faic an caibideil |