Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:18 - Littafi Mai Tsarki

18 “Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 “Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:18
14 Iomraidhean Croise  

Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne,


Fir'auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”


Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.


Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.


A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.


A hannunka kuma ya ba da dukan wurare inda 'yan adam, da dabbobi, da tsuntsaye suke zama. Ya sa ka ka mallake su duka. Kai ne kan zinariyan nan na mutum-mutumin.


Suka amsa, suka ce, “Bari sarki ya faɗa wa barorinsa mafarkin, mu kuwa za mu yi maka fassararsa.”


Yanzun nan aka kawo mini masu hikima, da masu dabo don su karanta wannan rubutu, su kuma bayyana mini ma'anarsa, amma sun kāsa faɗar ma'anar rubutun.


Sai dukan masu hikima na sarki suka shigo, amma ba wanda ya iya karanta rubutun balle ya faɗa wa sarki ma'anarsa.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan