Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 “ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:17
30 Iomraidhean Croise  

Babu wani kamar Ahab da ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Matarsa, Yezebel, ita ce ta zuga shi.


Duk da wannan wahala da sarki Ahaz yake sha a wannan lokaci, sai ƙara rashin aminci yake yi ga Ubangiji.


Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama, Shi yake sarautar duka.


Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga, Suna ta yabon abin da yake mugunta.


Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci, Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.


Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.


Suna ta kiran junansu suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne! Ɗaukakarsa ta cika duniya.”


Sai na ji Ubangiji yana cewa, “Wa zan aika? Wa zai zama manzonmu?” Sai na amsa na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”


Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”


Zan kawo al'ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu ƙarfi ta ƙare. Za a ƙazantar da masujadansu.


“Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.


Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari'a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi.


Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne.


Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin yă shafe abubuwan da suke akwai.


Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala'iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.


Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”


Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan