Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “ ‘A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:14
19 Iomraidhean Croise  

Ba wanda zai tuna da shi, mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba. Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai. Za a sare mugunta kamar itace.


‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.


Ku gudu daga cikin Babila, Bari kowa ya ceci ransa, Kada a hallaka ku tare da ita, Gama a wannan lokaci Ubangiji zai sāka mata, Zai sāka mata bisa ga alhakinta.


Mun ba Babila magani, amma ba ta warke ba. Bari mu ƙyale ta, kowannenmu ya koma garinsu, Gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo har samaniya.


“Domin haka Ubangiji Allah ya ce, Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa,


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


Mai shela ya ta da murya da ƙarfi, ya ce, “An umarce ku, ya ku jama'a, da al'ummai, da harsuna mabambanta,


Yana da ganyaye masu kyau Da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.


Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.


Bayan wata goma sha biyu, sa'ad da yake yawatawa a kan benen fādar Babila,


Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.


Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.


Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.


Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”


ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa.


Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ta zama mazaunin aljannu, Matattarar kowane baƙin aljani, Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan