Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:13 - Littafi Mai Tsarki

13 “ ‘A cikin wahayin da na gani sa'ad da nake kwance a gado, sai ga wani mai tsaro, tsattsarka, ya sauko daga sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 “A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:13
18 Iomraidhean Croise  

Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye, Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,


Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku, Ku da kuke biyayya da umarnansa, Kuna kasa kunne ga maganarsa!


Ana girmama ka a cikin majalisar talikai, Duk waɗanda suke kewaye da kai suna yin tsoronka ƙwarai.


“ ‘Wahayin da na gani ke nan sa'ad da nake kwance a gadona. Na ga wani itace mai tsayi ƙwarai a tsakiyar duniya.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.


Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni.


A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa'ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa.


Waɗannan manyan dabbobi guda huɗu, sarakuna ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.


“Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.


Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”


Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa'an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!


“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.


yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Ya ce, “Ubangiji ya taho daga Sina'i, Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka, Ya taho tare da dubban tsarkakansa, Da harshen wuta a damansa.


Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,


zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala'iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan