Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 4:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Yana da ganyaye masu kyau Da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 4:12
13 Iomraidhean Croise  

Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye, Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,


“Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare, Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.


In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.


Shi wanda muke dogara gare shi, Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu, Shi wanda muka ce, “A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”


A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shi Don ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya, Ya zama itacen al'ul na gaske. Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa, Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.


Su kuma suka gangara tare da shi zuwa lahira, suka tarar da waɗanda aka kashe da takobi, wato waɗanda daga cikin al'ummai suka yi zama a inuwarsa.


Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “ ‘A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.


Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”


“Amma fa wannan rana ko wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da suke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.


duk da haka in an shuka ta, sai ta girma ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”


Kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa, ta kuma girma ta zama itace, har tsuntsaye suka yi sheƙarsu a rassanta.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan