Daniyel 4:1 - Littafi Mai Tsarki1 “Daga sarki Nebukadnezzar zuwa ga dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta waɗanda suke zaune a duniya duka. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20201 Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Faic an caibideil |
Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama'a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki.
A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.