Har ma ya ga a kashe Mordekai kaɗai, wannan bai isa ba. Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya nema ya hallaka dukan Yahudawa, wato kabilar Mordekai, waɗanda suke a dukan mulkin Ahasurus.
su kasance samari ne kyawawa, waɗanda ba su da wata naƙasa, masu fasaha cikin kowane abu, masu fahimta, da masu saurin ganewa, waɗanda suke da halin iya hidima a fādar sarki. Nebukadnezzar ya umarci Ashfenaz ya koya musu littattafan Kaldiyawa da harshen Kaldiyawa.
Sa'an nan Kaldiyawa suka amsa wa sarki, suka ce, “Ba wani mahaluki a duniya wanda zai iya biyan wannan bukata ta sarki, gama ba wani sarki wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya a wurin mai sihiri, ko mai dabo, ko Bakaldiye.
Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.
Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.
Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci.