Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:7
15 Iomraidhean Croise  

Babila ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, Ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashen duniya sun sha ruwan inabinta, suka haukace.


Sarki Nebukadnezzar kuwa ya fāɗi a gaban Daniyel, ya gaishe shi, sa'an nan ya umarta a miƙa hadaya, da hadaya ta turare ga Daniyel.


Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya.


Mai shela ya ta da murya da ƙarfi, ya ce, “An umarce ku, ya ku jama'a, da al'ummai, da harsuna mabambanta,


cewa sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi, ku yi sujada ga gunkin zinariyan nan da sarki Nebukadnezzar ya kafa.


Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.”


A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa.


Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al'ummai su yi yadda suka ga dama.


Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.


Ɗaya daga cikin kawunanta, an yi masa rauni kamar na ajali, amma rauninsa mai kamar na ajalin nan ya warke. Sai dabbar ta ɗauke wa duk duniya hankali, suna mamaki,


Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.


Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan