Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:6
20 Iomraidhean Croise  

ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”


Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la'ana cewa, ‘Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!’


Sai sarki ya amsa wa Kaldiyawa, ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini da mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa gunduwa, a mai da gidajenku juji.


Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.


Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”


Sai aka ɗaure su suna saye da rigunansu da wandunansu, da hulunansu, da sauran tufafinsu, aka jefa su a tanderun gagarumar wuta.


Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.


Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.


Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da 'yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki.


su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.


su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”


Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”


Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi umarni a kawo kan Yahaya. Ya tafi ya fille wa Yahaya kai a kurkuku,


Hayaƙin azabar nan tasu ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato, waɗannan masu yi wa dabbar nan da siffarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”


Ya kuwa buɗe ramin mahallakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan