Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 cewa sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi, ku yi sujada ga gunkin zinariyan nan da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:5
5 Iomraidhean Croise  

Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne, Da hannu aka siffata su.


Sarki Nebukadnezzar kuwa ya fāɗi a gaban Daniyel, ya gaishe shi, sa'an nan ya umarta a miƙa hadaya, da hadaya ta turare ga Daniyel.


Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya.


Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”


Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan