Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Mai shela ya ta da murya da ƙarfi, ya ce, “An umarce ku, ya ku jama'a, da al'ummai, da harsuna mabambanta,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:4
13 Iomraidhean Croise  

A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.


Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima, Ki faɗi albishir! Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona, Ki faɗi albishir! Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro. Ki faɗa wa garuruwan Yahuza, Cewa Allahnsu yana zuwa!


Ubangiji ya ce, “Ku yi kuka da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa! Ku ta da muryoyinku kamar busar ƙaho. Ku shaida wa jama'ata laifinsu, ku shaida wa zuriyar Yakubu zunubansu.


Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya.


Sai hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna suka taru don keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Suka kuma tsaya a gaban gunkin.


Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.


“Daga sarki Nebukadnezzar zuwa ga dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta waɗanda suke zaune a duniya duka. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!


Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “ ‘A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.


Dariyus sarki kuwa ya rubuta wa dukan jama'a da al'ummai, waɗanda suke zaune a duniya duka, ya ce, “Salama ta yalwata a gare ku.


An danne Ifraimu, shari'a ta murƙushe ta, Domin ta ƙudura ta bi banza.


Domin kun kiyaye dokokin Omri, Kun bi halin gidan Ahab, Kun kuma bi shawarwarinsu. Domin haka zan maishe ku kufai, In mai da ku abin dariya, Za ku sha raini a wurin mutanena.”


Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa, “Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan