Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Sa'an nan sarki ya ƙara wa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego girma a lardin Babila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:30
9 Iomraidhean Croise  

Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.


Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata, Zan kiyaye waɗanda suka san ni.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.


Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila.


Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”


Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan