Daniyel 3:25 - Littafi Mai Tsarki25 Sarki ya ce, “Amma ina ganin mutum huɗu a sake, suna tafiya a tsakiyar wuta, ba kuma abin da ya same su, kamannin na huɗun kuwa kamar na ɗan alloli.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202025 Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.” Faic an caibideil |
Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.