Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Sa'an nan mutanen nan uku, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka faɗi a tanderun gagarumar wuta a ɗaure.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:23
13 Iomraidhean Croise  

Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.


Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi, Zan kasance tare da ku, Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba. Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba, Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.


Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Sarki Nebukadnezzar kuwa ya zabura ya miƙe tsaye, cike da mamaki. Ya ce wa manyan fādawansa, “Ashe, ba mutum uku ne muka jefa a wuta ba?” Su kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ba shakka, haka yake, ranka ya daɗe.”


Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan