Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Tsananin umarnin sarki ya sa aka haɓaka wutar, sai harshen wutar ya kashe waɗanda suka jefa su Shadrak, da Meshak, da Abed-nego cikin wutar.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:22
10 Iomraidhean Croise  

ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba.


Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, “Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba.”


Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.


Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Daniyel ya ce wa Ariyok shugaban dogaran sarki, “Me ya sa ake gaggauta dokar sarki haka?” Sai Ariyok ya bayyana wa Daniyel yadda al'amarin yake.


Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.


Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.


Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, ya yi ta tuhumar masu tsaron, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa'an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi 'yan kwanaki a can.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan