Daniyel 3:20 - Littafi Mai Tsarki20 Sa'an nan ya umarci waɗansu ƙarfafan mutane daga cikin sojojinsa su ɗaure Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, su jefa su a tanderun gagarumar wuta. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202020 Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar. Faic an caibideil |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”