Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:19
26 Iomraidhean Croise  

Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā.


Sa'ad da Haman ya ga Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba, sai ya husata.


Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi.


Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.


Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.


Ba kalmar da ta fi “fāɗin rai” dacewa ga mutum mai girmankai, mai fāriya marar tunani.


Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku, Su waɗanda suka sa kuka kwanta a tituna Suka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”


Saboda haka sarki ya husata ƙwarai, ya umarta a karkashe duk masu hikima na Babila.


Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki.


Sa'an nan ya umarci waɗansu ƙarfafan mutane daga cikin sojojinsa su ɗaure Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, su jefa su a tanderun gagarumar wuta.


Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.


Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.


“Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku.


“Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku.


sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku.


sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.


Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su.


Da suka ji haka, suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan