Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:17
34 Iomraidhean Croise  

A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.


Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”


Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi? Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa, Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum?


Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai, Ba muguntar da za ta taɓa ka.


Allahnmu yana Sama, Yana aikata yadda yake so.


Ubangiji yakan ceci adalai, Ya kiyaye su a lokatan wahala.


Yakan taimake su, yă kuɓutar da su, Yakan cece su daga mugaye, Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.


Ya Ubangiji, kamar mafarki suke Wanda akan manta da shi da safe, Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.


Allah ne Mai Cetona, Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba. Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi, Shi ne Mai Cetona.”


Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki. Za ki tsira daga shan zalunci da razana. Gama ba za su kusace ki ba.


Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai, Zan kiyaye ka. Ni Ubangiji na faɗa.”


Zan maishe ka garun tagulla saboda waɗannan mutane, Za su yi yaƙi da kai, amma ba za su yi nasara a kanka ba, Gama ina tare da kai don in cece ka, in kuɓutar da kai.


Zan kuɓutar da kai daga hannun mugaye, Zan ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”


Nebukadnezzar fa ya matso kusa da ƙofar tanderun gagarumar wuta, ya ce, “Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, bayin Allah Maɗaukaki, ku fito, ku zo nan!” Sai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka fita daga cikin wutar.


Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’


Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.”


Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa.


Yakan yi ceto, yakan kuma kuɓutar, Yana aikata alamu da mu'ujizai a sama da duniya. Shi ne wanda ya ceci Daniyel daga bakin zakoki.”


Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji, Zan jira ceton Allahna, Allahna zai ji ni.


Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”


Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.


Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.


Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.


Ubangiji wanda ya cece ni daga dāgin zaki da na beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafiliste.” Sa'an nan Saul ya ce wa Dawuda, “Tafi, Ubangiji ya taimake ka.”


A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra'ila.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan