Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:16
4 Iomraidhean Croise  

Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”


Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan