Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:15
25 Iomraidhean Croise  

Daga cikin dukan allolin ƙasashe, wane ne ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannuna har da Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?’ ”


Amma ina roƙonka ka gafarta zunubansu, in kuwa ba haka ba, ina roƙonka ka shafe sunana daga cikin littafin da ka rubuta.”


Amma Fir'auna ya ce, “Wane ne Ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar Isra'ilawa su tafi? Ai, ban san Ubangiji ɗin nan ba, balle in bar Isra'ilawa su tafi.”


Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba'a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra'ila.


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Idan ba ku tuno mini da mafarkin ba, hukuncin kisa ne yake jiranku. Kun haɗa kai don ku yi mini maganganun ƙarya na wofi har lokaci ya wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”


Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.


Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.”


Da ya zo kusa da kogon da Daniyel yake, sai ya ta da murya ya yi kira da damuwa, ya ce wa Daniyel, “Ya Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta masa kullum, yana da ikon cetonka daga zakoki?”


A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin.


Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”


Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.


Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,


In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”


Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.


Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.


Da duk waɗanda suke zaune a majalisar suka zura masa ido, suka ga fuska tasa kamar fuskar mala'ika take.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan