Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:12
15 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.


Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma duk da haka bai kai ga kishi ba.


Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.


Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.


Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.


Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari.


Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”


Sa'an nan sarki ya ƙara wa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego girma a lardin Babila.


Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”


Sa'ad da sarki ya ji wannan magana, sai ransa ya ɓaci ƙwarai, sai ya shiga tunani ta yadda zai yi ya kuɓutar da Daniyel. Ya yi ta fama har faɗuwar rana yadda zai yi ya kuɓutar da shi.


har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”


ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan