Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 3:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 3:11
6 Iomraidhean Croise  

Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya.


Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”


Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.”


Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”


Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da 'yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki.


“Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan