Daniyel 3:1 - Littafi Mai Tsarki1 Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20201 Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon. Faic an caibideil |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.